Al'umma da yawa suna kokawa bisa wannan al'amari dake shirin faruwa na dakatar da bankuna karɓar tsofin kuɗaɗe da gwamnatin Tarayya take shirin yi a ƙarshen watan junairu, wanda ya kama 31/01/2023. Wannan batu dai ya biyo baya ne bayan da Buhari da Emefiele shugaban bankin ƙasa suka tattauna a tsakanin su kuma suka fitar da rana da lokaci ba tare da neman shawara ko yardar wasu ƴan ƙasa ba kamar yadda tsarin Dimokaraɗiyya ya bayyana.
A wannan gaɓa ne muka tuntuɓi Mal. Dr. Sa'eedu Dukawa malami a jami'ar Bayero dake Kano, inda ya bayyana mana cewa: tun farko an take tsarin dimokaraɗiyya wajen yanke hukuncin dena karɓar kuɗi ba tare da tuntuɓar ƴan ƙasa ba, sannan babu isassun kuɗi da zai wadatu al'umma kamar yadda sukai iƙirarin maye gurbin tsaffin da zasu karɓa, saboda haka muddin aka hana ƴan kasuwanni da bankuna karɓar tsohon kuɗi a lokacin da suka kayyade, to fa da yiwuwar a samu tashin hankalin da ba'a taɓa tsammani ba. Domin wannan harka ce ta rayuwar mutane ba wani abu daban ba.
A ƙarshe ya ƙara da cewa akawai zargin tanadi na cuzgunawa jam'iyyar adawa a wannan kakar zaɓe da ake ciki.