Kungiyar Al Nassr ta soke kwantiragin Vincent Aboubakar na Kamaru don maye gurbinsa da Cristiano Ronaldo.
A bisa ka’idojin gasar lig-lig ta kasar Saudiyya, kungiya na da damar daukar ‘yan wasan kasashen waje 8 kacal, kuma Al-Nassr na da adadin 'yan wasan kasashen wajen, don haka ya zama dole dan wasa daya ya tafi domin Ronaldo ya samu gurbin buga mata kwallo.
Rahotanni na cewa an cimma yarjejeniya da Aboubakar kan ya karbi wasu kudade masu tsoka don ya janye wa Ronaldo.