Duk wanda yake son yin takara, ya je ya nema. Muna da jam'iyyu guda 18 wanda INEC ta yarda da su. In jam'iyyarka ta baka dama, ka shiga gari ka sadu da jama'a, su kuma su zabeka.
Haka aka yi a zaben farko na 1954. Haka aka yi a zabe na biyu 1959. A zaben 1979 haka aka yi. Haka aka yi a zaben 1992. A jamhuriya da muke ciki ta 1999 shekara 23 haka ake yi.
A lokacin da arewa tana matsayin lardi basu taba zama a jam'iyyar siyasa daya ba a dunkulalliyar Najeriya. Haka da aka raba Najeriya gida 12, aka sake rabata gida 19, aka yi jihohi 30, aka yi 37 har da Abuja. A jamhuriya ta farko arewa sun yi NPC da NEPU. A jamhuriya ta biyu sun yi NPN da PRP da GNPP har da NPP. A jamhuriya ta uku sun yi SDP da NRC. A wannan jamhuriyar yanzu suna cikin jam'iyyun jama'a guda 18.
Arewa yanki ne mai 'yanci da walwala a siyasa. Ba a tilasci, amma mutanen yankin suna daukar saiti daya idan zabe yazo. Kowa da yake takara yana shiga zabe, ranar kada kuri'a sun san inda suke jefata. A zabukan da aka yi na tarayya a 1959 wakilai da zasu je tarayya a Lagos mafi rinjayensu NPN suka yi, haka a 1979 NPN suka yi a matakin kasa. A 1992 SDP suka yi a matakin kasa. A 1999 PDP suka yi a matakin kasa. A 2007 PDP suka yi. A 2015 suka yi APC wacce ta hada ko ina na Najeriya.
Daga arewa an yi Tafawa Balewa da Sardaunan Sakkwato a NPC, a gefe daya kuma ga Mallam Aminu Kano a NEPU da JS Tarka a UMBC. A arewan an yi Shehu Shagari a NPN, Waziri Ibrahim a GNPP , Aminu Kano a PRP. A arewan an yi Bashir Tofa a NRC. A arewan an yi Buhari a ANPP a shekarar 2003, an yi Buhari da Umaru Musa Yar Aduwa da Atiku Abubakar a 2007. A arewan an yi Buhari da Nuhu Ribadu da Mallam Shekarau a 2011. A arewan kowa ma ya yi Buhari a 2015, yanzu ma a 2023 a arewan akwai Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso. Wannan ba sabon abu bane.
Mutanen arewa a duk lokacin kakar zabe ta zo na duk kasa, masalahar da suke dauka ita ce, wanda ya fito daga yankinsu, kuma a al'adarsu basa kin baiwa wanda suke so kuri'a, ko zai yi nasara ko ba zai yi ba, sai dai hukuncin da sukan yi, yafi rinjaye a inda suke yakini da zato mai karfi. Misali sun fi zaton nasara ga Shagari, amma sun zabi Aminu Kano da Waziri Ibrahim. Sun fi zaton nasara ga Mashood Abiola, duk da haka sun zabi Bashir Tofa. Sun fi sa rai ga Obasanjo a 1999 kuma suka zabe shi, duk da cewa da yawa an zabi Olu Falae. Sun watsar da Atiku Abubakar suka zabi Yar Aduwa a 2007. Sun ki zabar Shekarau da Ribadu a 2011 suka zabi Buhari.
Ban sani ba, shin a bana za su canja dabi'ar da aka sansu da ita, su kafa wani sabon tarihin ?. Allahu a'alam.
Daga Bashir A Bashir
Shafin Raihana.com.ng