Allah Ya yiwa jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Abdulwahab Alhassan (Awarwasa), rasuwa a yau Litinin, 23 ga watan Janairu 2023.
Kafin rasuwar jarumin yataka rawa cikin shirin fina-finai masu dogon zango kamar aduniya, sanda, danjarida da dai sauransu
Wata majiya mai ƙarfi ta tabbatar mana da cewa ya mutu da muradin yin aure a rayuwar sa amma bai samu damar yi ba har Allah ya karɓi ransa, sai dai akwai wata budurwar sa da suke da muradin aure tsakanin su.