Yan bindiga sun kai hari tashar jirgin ƙasa da ke ƙaramar hukumar Igueben a jihar Edo tare da yin garkuwa da fasinjoji masu yawa.
Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da fasinjojin ke shirin hawa jirgin ƙasan zuwa garin Warri da ke jihar Delta
Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Edo Chidi Nwabuzor, ya ce kawo yanzu ba su samu labarin rasa rai ba.
To sai dai ya tabbatar da cewa wasu fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga daga maharan.