Wata kotun majistare a Kano, karkashin jagorancin mai Shari'a Jostis Mustapha Sa'ad Datti, ta tura da mutumin nan mai suna Tasiu Abdullahi Hayin Hago, zuwa gidan ajiya da gyaran hali, sakamakon rashin cika ƙa'idar beli.
Jami'an yan sanda ne suka samu nasarar cafke Tasiu Abdullahi mai shekaru 45, tare da katunan zaɓe na din-din-din (PVC) guda 29, wadanda dukkansu mallakin mutanen karamar hukumar Dawakin Tofa ne a jihar Kano, inda ya bayyana cewa, Abba Ganduje ne yake sa shi ya karɓo.
Mai Shari'a ya dage cigaba da sauraron Shari'ar, har zuwa ranar 30 ga watan da muke ciki na Janairu, tare da umarnin a cigaba da tsare shi a gidan ajiya da gyaran hali.