Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam'iyyar
SDP Yarima Adewole Adebayo ya kawo ziyara jihar kano, inda ya ƙaddamar da manufofin sa tare da ziyartar masarautun jihar kano domin nuna girmamawa garesu. Ɗan takarar wanda ya samu tarbar
Hon. Bala Muhammad Gwagwarwa
wanda ke takarar gwamna a kano ƙarƙashin tutar jam'iyyar ta SDP shima ya bayyana irin nashi ƙudirce -ƙudircen na kawowa kano sauyi musamman sashen kasuwanci gyara domin a samu rayuwa mai inganci. Ka zaluka Yarima ya bayyanawa al'umma irin nashi manufofin na wanda suka haɗar da KAWO ƘARSHEN TALAUCI DA RASHIN TSARO.
A ƙarshe
Yarima yace gwamnatin su irin wadda su
Malan Aminu kano suka gabatar a baya da kuma yadda suka umarce su suyi wato gwamnati domin al'umma haka zasu gudanar da tsarin mulkin su idan Allah ya basu dama.