Ƴan ƙungiyar Vigilantee sun fasawa wata Amarya
ido a kano, yayin da take tsaka da shagalin biki
Ƴan Kwamiti wato Yan Vigilante sun Fasa mata Ido lokacin da take tsaka da Shagalin Bikinta a Unguwar kwajalawa Dan Tamashe Karshen aiki.
Amarya Khadija Abdullahi
ta bayyanawa wakilin mu yadda aka buga mata makami a idon ta yayin da take tsaka da gudanar da bikin nata.
Hajara
wadda ke zama Mahaifiyar ta ta bayyana yadda suka jefa ƴarsu a cikin bala'i kuma sun buƙaci hukuma su bi musu haƙƙin su Kamar yadda Shima Mahaifin ta ya bayyana.
Abdu Mu'azu wanda aka fi dani da
baƙo ɗan kasuwa.
Shima angon amaryar Mustapha Bala ya bayyana cewa mai unguwar garin bai son a ɗauki mataki a kan abunda ƴan vigilantin sukai, kuma yanzu haka Amaryar tana gadon asibiti suna kula da ita.