Alh. Sani kwangila Yakasai shugaba kamfanin Kwangila na SKY ya bayyan farin cikin sa dangane da gayyata ta musamman daya samu daga hukumar wannan makaranta mai albarka inda nan take ya bada jimillar kuɗi nera 500,000 a matsayin gudunmawa ta musamman da kuma hidima ga alqur'ani maigirma. Shima a nashi jawabin shugaban Makarantar yayi kira ga masu hannu da shuni kan su dunga zuba jari a fannin addini domin samun tagomashi a wajen Allah (S.W.A). Malam Dr. Umar Muhammad Ƙani malami ne a makarantar Legal kuma malami ne a wannan islamiya ya kuma bayyana tasirin alqur'ani maigirma a zukatan matasa musamman mata domin su ke koyar da tarbiyya ta yau da gobe.
An yaye Ɗalibai 136. 102 Mata, 36 Maza.
January 08, 2023
0
Saukar alqur'anin wadda aka gabatar Yau 07/01/2023. a Ɗiso qtrs Ƙaramar Hukumar Gwalen Jihar Kano. Inda aka yaye ɗalibai kimanin 136 ciki da akwai Maza 34 Mata 102.
Tags