Anyi ba ai ba idan an kai kuɗi ba zasu fita ba har zuwa 10 feb. ~ I.G MARYAM.
idan masu karatu suna bibiyar mu sun sani cewa babban bankin kasa ya saka ranar da za'a dena karɓar tsofaffin kudade wanda hakan ya jawo cece kuce da korafe-ƙorafe a gari mutane nna ganin bai kamata ba musamman duba da yadda mutanen suka shiga tashin hankali da firgici. I.G MARYAM yana daga cikin manyan masu ƙungiyoyin fararen hula a ƙasa ya kuma bayyana yadda wannan lamari zai yi tasiri a tsakanin al'umma. ''Yanzu wannan kudin da aka dena karba ko ake shirin dena ƙarba ya jawo mutane suna tunanin dena zaɓe saboda yadda suka yarda da shugaba Muhammadu Buhari amma ya watsa musu ƙasa a fuska domin a tunanin su idan sukaa yiwa wani irin yadda sukai wa Buhari shima zai watsa musu kasa a fuska, wannan canjin kuɗi da akai da kuma ƙara lokaci aikin banza ne saboda idan kuka kai kuɗi baza su fita ba kuma baza a basu sabbin da ake fadar za'a basu ba, misali kana kashe 50,000 kullum amma ance 20,000 kawai za'a ke baka, ina amfanin baɗi ba rai?.''