Auwal Olu Dakata ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP mai alamar kayan marmari inda ABBA GIDA-GIDA ɗan takarar gwamna a Kano ƙarƙashin tutar jam'iyyar NNPP ya karɓe shi, ƙarƙashin Jagorancin JAGORA Alh. Mal. Mustapha Garba Maisikeli.
Auwalu Olu Dakata yq bayyana jam'iyyar NNPP a matsayin wata kafa ta taimakon al'umma da kuma tseratar dasu daga bala'i inda ya kwatanta ta da JIRGIN ANNABI NUHU (A.S). Shima JAGORA Alh. Mustapha Garba Maisikeli ya nuna farin cikin sa bisa wannan lamari da kuma gano gaskiya da Olu yayi tun kafin dare yayi masa ya kuma ce babu mai iya zama a jam'iyyar su ta NNPP sai mai kishin Talaka da kuma yiwa Talaka fatan samun sauƙi a rayuwa. A ƙarshe ɗan takarar gwamna ABBA yace ƙofa a buɗe take har yanzu ga waɗanda sukai niyyar shiga jam'iyyar su domin samawa Talaka sauƙi a rayuwa cikin ikon Allah ya kuma yi addu'ar Allah ya basu Nasara a zaɓen shekarar 2023.