Akwai yiwuwar a dakatar da haƙar man fetir a arewacin najeriya muddin aka samu sabon shugaban ƙasa daga kudancin ƙasar nan. Tun lokacin mulkin su
Tafawa Balewa aka gano cewa akwai man fetir a arewacin ƙasar nan amma kasancewar wannan lokacin babu tunanin za'a zo irin wannan taƙi na nuna bambanci tsakani sai ya kasance aka fi baiwa ɓangaren kudancin kasar muhimmanci na haƙo ɗanyen man fetir, su kuma arewaci sai aka fi bada himma wajen noma kiwo da sauran su. Akwai batun cewa jihar
Bauchi koma dai
Gombe nada wannan arziƙi a ƙasa daga baya dai sunyi niyyar fara wannan aiki amma sai aka hamɓarar da gwamnatin su
Sardauna kuma aka kashe su inda gwamnatin soji ta karɓi kasar karkashin jagorancin Gen. Aguyi ironsi wanda inyamuri ne kuma shine karo na farko a faɗin ƙasar najeriya don haka aka dena waccan magana kuma aka hau kashe arewa da manyan ta ko ta halin ƙaƙa. Bayan hamɓarar da gwamnatin sa ne aka shiga yaƙin basasa na tsahon lokaci ƙarƙashin mulkin Gen. Yakubu Gawon wanda bai ji daɗin mulkin ba kuma bayan da
Gen. Murtala Muhammad Ramat ya karba sai ya fara makamancin wannan yunƙuri amma bai jima ba aka kashe shi saboda tsantsar rashin yarda da rashin gaskiya ko cin amana da kuma niyya ta gyara ƙasar musamman arewacin najeriya. A lokacin mulkin
Gen. Sani Abacha ne aka samu yayi jan wuya kuma ya bugi ƙasa tare da alwashin sai ya hako wannan ɗanyan mai na arewacin najeriya a sannan ne aka fara aiki karo na farko na haƙo man shima sai da aka ga bayan sa, kuma bayan ya shuɗe sai aka dena zancen haƙo man domin
Gen. Olushegun Obasanjo shine wanda ya samu cikakkaliyar damar haƙo wannan man amma sai ya hana kuma yasa aka rufe gurin ba iya nan ya tsaya ba sai da ya kashe duk wata babbar masana'anta a arewacin najeriya kuma yayi duk mai yiwuwa wajen ganin ya gina garin su (Mahaifar sa) wato Enugu inda ya kai musu wutar lantarkin da idan aka bamu kaso ɗaya cikin goman wadda ya kai garin, ya ishe mu mu fita daga ƙangin rashin wutar lantarki. Ba don komai yayi haka ba sai don kiyayya da yakewa arewacin najeriya. Shuga Umaru Musa Ƴar'adua yayi wannan yunƙuri cikin agenda 7 daya tsara gabatarwa amma rai yayi halin sa babu zancen babu tashin zancen. Shima shugaba
Goodluck haka yayi ya gama ya tafi bai yi maganar gurin ba duk a cikin irin ƙiyayya ko rashin son ganin arewacin najeriya ta samu wannan ɗanyan mai. Sai a yanzu lokqcin shugaba
Muhammad Buhari wanda shima a ƙurarren lokaci yayi wannan yunƙuri domin a cikin rijiya uku da ake dasu yanzu a arewacin najeriya akwai guda ɗaya wadda shugaba
Gen. Sani Abacha ya gina wadda babu komai a ciki face tarkace da ƙura a ciki. Har yanzu dai aikin ake amma kuma muddin aka zaɓi shugaba daga kudu to la shakka babu da yiwuwar a dakatar da wannan aikin domin anyi baya an gani. Zamu zo muku da kashi na biyu na cikin wannan hira ta musamman da mukayi tare da
Cmr. Adam Dakata,
domin jin ya take kayawa tsakanin mutanen jihar Gombe da Bauchi kan rikicin iyaka da ake haƙo wannan ɗanyen mai, domin akwai kwantacciyar rigima ta cikin gida.