~ mijin Æ´ar gidan Ganduje
Mijin Æ´ar gidan gwamnan Kano, Asiya Balaraba Ganduje, Inuwa Uba, ta hannun lauyansa, Barista Umar, ya ce batun Shari'arsu ya wuce maganar dawo da sadaki, domin wanda yake karewa na da sharudda game da wasu abubuwa da ya mallaka, bayan maganar sadakin.
A yau aka cigaba da sauraron Shari'ar a babbar kotun shari’ar Musulunci da ke Kano, inda kotun tayi watsi da karar farko da lauyan mijin Balaraba ya shigar, yana kalubalantar hurumin sauraran karar raba aurensu.
Balaraba ce dai ta shigar da karar mijin nata, Inuwa Uba, ta hannun lauyanta, Barista Ibrahim Aliyu Nassarawa, tana rokon kotun ta raba aurensu ta hanyar Khul’i, saboda ta gaji da zama da shi.
Ta kuma bukaci kotun ta ba ta damar biyansa sadakinsa na N50,000 da ya biya lokacin aurensu, amma kuma mijin yace a shirye suke su yi sulhu da Balaraba.
Barista Umar, ya ce bai san nawa ne ainihin sadakin ba, daga nan ne kuma Alkali Halliru Abdullahi ya ba wa bangarorin biyu umarnin komawa su tabbatar daga ma’auratan, tare da dage zaman shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Janairu don jin ainihin kudin sadakin.