Hukumar dake umarni ga aikata kyakykyawan tare da hani ga aikata mummunan aiki ta jihar Kano (HISBAH) ta sanar da cewa ta samu nasarar cafke wani mai suna Kamalu Bashir, bisa yin rawa ta wuce Hankali a Shafin sada zumunta na TikTok.
Babban jami'i a sashin yada labarai da fasaha na hukumar, Sani Zailani, ne ya sanar da haka, inda yace, babban kwamandan Hisbah Dakta Muhammad Harun Sani ibn Sina yace hukumar ba zata lamunci abubuwan fitsara a kafafen sada zumunci.
A yayin nasiha da tsawatarwa daga babban kwamanda da mataimakansa sun nuna rashin jin dadinsu irin yadda ya je fa kansa cikin fitina da lalacewar tarbiyyar, mussamman kasancewar Kamalu dan Kano ne.
Yace, hukumar Hisbah zata dauki matakin da ya dace akansa da masu aikata abinda yasaba da Shari'a da bata tarbiyya, har da ita Fati yobe abokiyar rawar tasa da ta gudu garinsu.
Daga karshe hukumar tayi mishi nasiha damage tsoratar dashi akan tanadin da addinin muslunci yayiwa nasu yada fasadi ranar gone kiyama