*MALAM LAWAN TRIUMPH*
*Budadiyar Wasika Zuwa Ga Malam LAWAN Triumph,✍️ Hakika Munsheda Cewa Kai Malamine Amma Kana Wasu Abubuwa Kana Neman Kabata Rawarka Da Tsallake Ya Malam, Kana Neman Kadau Wani Bangare Na Siyasa Kanuna Kamar Kana Goyan Bayan Wayansu,
Malam Lawan Triumph Muna Kira Gareka Acikin Ladabi Da Biyayya Sannan Kuma Da Girmamawa Irin Wanda Addinnin Muslinci Yayi Umarni Ayiwa Duk Wani Malami Biyayya,
*Malam Akan Magana Dakake Cewa Mu Yan Kwankakwasiyya Bamuda Tarbiya Kuma Bama Girmama Manya To Wannan Kalma Taka Akan Yan Kwankakwasiyya Kawai Take Aiki Kuma Acikin Satin Nan kakara Fitowa Ka Maimaita Kuma Kana kirarin Cewa Sokake Ka Gyara Siyasar Kano Saboda Adena Cin Mutunci Acikin ta Kuma Bayan Gyaran Iya Akan Yan Kwankakwasiyya Kakeyinsa Wannan Shine Yake Nunawa Baka Kaunar Kwankakwasiyya Da Duk Wanda Yake Cikin Ta,
A Kwanakin Baya Akwai Wani Dan Siyasa Daya Fito Gidan Radio 📻 Yaci Mutuncin ( Sheikh Aminu Daurawa ) Yace Ba Malami Bane Asalima Tambayar Dayake Amsawa Saiyaje Gida Ya Rubutata Sannan Yake Zuwa Ya Amsa A Radio 📻 A Lokacin Malam LAWAN TRIUMPH Maiyasa Baka Fito Kayi Masa Nasiha Ba Kamar Yadda Kakeyiwa Yan Kwankakwasiyya Kuma Tinda Malami Yataba, Amma A Shekarun Baya Saboda Anyiwa Malam Isah Ali pantami Rashin Kyautawa Haka Kafito Kadinga Caccakar Yan Kwankakwasiyya Kaga Wannan Alama Ce Ta Kadauki Bangare Kenan,
*Shekarun Baya Akwai Wani Shugaban Jam,iya Daya Fito Yace Koda Tsiya_Koda Tsiya Saisun Ci Zabe Kuma Yakara Dacewa Idan Anga Dan Kwankakwasiyya To Adakeshi Andaki Banza Babu Abinda Za,ayi MALAM LAWAN TRIUMPH A Lokacin Munjika Shiru Baka Fito Kayi Magana Amma Yanzu Ansamu Sabani Da Wata Baiwar Allah Mace Amma Munjika Kafito Kana Allah Wadai Da Abinda Akayi ?
Muna Kira Ga Malam Dan Allah Yadinga Kokari Yana Fadar Gaskiya Ako Ina Domin Hakan Shine Zaisa Aci Gaba Da Kallon ka Amatsayin Malami Ba Dan Siyasa ba🙏🙏
Sign By Hassan Yahaya Zano.