Cibiyar Wayar da kan al'umma kan kyakykyawan shugabanci da Adalci, (CAJA). ta gabatar da taron wayar da kan ƴan takarkarun gwamnonin kano a ɗakin taro na ɗakin saukar baƙi na (Bristol), a ranar 12 ga wannan watan na junairu.
Taron wanda aka shirya shi domin yiwa ƴan takarkarun bita ta musamman kan kyakykyawan shugabanci a addinan ce da kuma yadda zasu gujewa kura-kurai bayan Allah ya baiwa ɗaya daga cikin su. Taron dai ya samu halartar Manyan Malaman addini inda suka gabatar takardu da dama masu jan hankali da tunasarwa sosai . Sai dai har aka kawo ƙarshen wannan taro babu Ɗan takarar Gwamna na ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC Nasiru Yusif Gawuna.
Ƴan takarkarun da suka samu damar halartar wannan taro sun haɗar da :
ABBA GIDA-GIDA (NNPP)
BASHIR I BASHIR (LP)
SALIHU TANKO YAKASAI (PRP)
Wakilin mu ya tuntuɓi shugaban wannan cibiya Cmr. Kabiru Dakata don jin ba'asin rashin zuwan wannan ɗantakara, inda ya bayyana cewa ''mun gayyace shi amma bai samu damar zuwa ba kuma bai faɗi dalili ba sai daga baya duk da cewa shine wanda ya saka ranar taron kuma aka yarda bisa sahalewar shi amma yaƙi zuwa''.
Ko me hakan yake nufi??.. ba zamu ce komai ba amma mun hangi Cmr. Kabiru Dakata yana faɗa a shafin sa na sada zumunta inda ya wallafa hotunan Ƴan takarkarun yana cewa ''InshaAllahu a cikin ku za'a sami gwamnan jihar kano''.