Taron ya gudana karkashin Jagorancin Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da mataimakinsa Dr Nasiru Yusif Gawuna,
Kamar su Kungiyar Izala Kungiyar Qadiriyya da Kungiyar Tijjaniya kan karancin sabon Kudi da yadda abun ya shafi rayuwar Al'umma a Jihar Kano.
Gwamnati da Malaman sunyi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamnan Babban Bankin 'kasa na CBN daya Kara wa'adin daina karbar Tsohon Kudin saboda rashin wadatar Sabon Kudin a Hannun al'umma.
Toni da hada-hadar kasuwanci yafara samun barazanar durkushewa a sassan kasar nan ciki kuwa harda Jahar Kano datake amsa sunan cibiyar kasuwanci.