Shugaban Kasar Najeriya Buhari yasha cifa da duwatsu a lokacin dayazo ziyarar bude wasu ayyuka da gwamnatin kano tayi
Inda wasu matasa suka yi Kone Kone tare da jefa manyan duwatsu akan hanyarsa ta wucewa.
Lamarin ya faru ne, yau Litinin a Lokacin bikin ƙaddamar sabuwar gadar sama ta Hotoro da ke jihar Kano.
Lamarin daya janyo jami'an tsaro suka runga harbin iska tare da cilla barkonun tsohuwa.
Sai dai wasu matasa yayin jifar tawagar shugaban kasar suna ihu suna cewa buhari yasa rayuwar talaka tayi tsada.