Matasa sunfi yarda da tsarin jagaliya maimakon maida hankali wajen ganin dukufa wajen tabbatarwa da kansu dama iyayen su abun alheri a rayuwa. Tun farko wasu ƴan siyasar mu sun taka rawa wajen gurɓata hankali da tunanin matasa wajen basu ababen da basu da kyau kuma suke amfani dasu abrayuwar su ta yau da gobe wasu ma suka maida shi jinin jikin su. Asibiti ya ƙara da cewa mafi yawan matasan mu baka ganin su a inda za'a inganta hankali da tunanin su sai dai waje saɓanin haka kamar dai siyasar da suke kuma ba ɓangare mai kyau ba sai dai ka gansu a ɓangaren jagaliya kasancewar siyasa tana da ɓangarori daban-daban.
Jaridar Raihana ta tuntuɓi Asibiti ko yana ganin akwai hanya da za'a bi don ganin an magance harkar jagaliya ta matasa a siyasa, da kuma hanyar da za'a bi domin a dawo da tunanin su hanyar da zata fishshe su.
Yace ''abu ne mai yawa kuma mai cike da ƙalubale wanda cire shi a cikin zukatan su keda wahala kuma domin sun rigada sun yarda a basu kuɗi wanda bai taka kara ya karya ba su kuma su je suyi abunda bai kamata ba, dole sai qn canza musu wannan tunanin kuma an nuna musu cewa hakan ba dai-dai bane, sannan a basu sana'a cikin taken ''da a baka kifi gwanda a nuna maka hanyar kama kifin''
A ƙarshe ya bayyana masu damar yiwa wannan tagomashi wato ƴan siyasa dasu duba Allah da manzon sa su taimakawa matasa wajen inganta rayuwar su maimakon ɓata musu ita.