DALIBAR JAMI'AR FUD TA CANZA SHARAR LEDAR RUWAN PURE WATER ZUWA KANANZIR DA MAN DIZEL.
Dalibar mai suna Zainab Bilyamin dake sashen tsangayar Chemistry na jami'ar tarayya dake Dutse ta mayar da sharar ledar ruwan pure water zuwa man fetir, kananzir da dizal a binciken da ta gabatar na kammala karatun ta na digiri, wato project.
An yiwa binciken nata taken" mayar da tsofin ledar pure water zuwa man fetur."
Mujallar Newsletter ta jami'ar ta tattara bayanan sakamakon binciken na ƙarshe inda ya nuna cewa man da aka samar daga samfurin ledar ta ruwan yana kama da kananzir da dizel na yau da kullum kamar yadda aka yi amfani da shi don kunna fitila mai amfani da kananzir da na'urar dake amfani da man dizel ba tare da wata matsala ba.
Mujallar jami'ar ta kuma gano cewa ana iya amfani da man fetur din wajen zubawa janareto a samar da wutar lantarki.
Zainab ta ce ta samu kwarin gwiwar ta gudanar da binciken ne bayan da ta karanta yiwuwar mayar da sharar ledar ruwan zuwa mai domin a Najeriya
sharar ledar na cika titina wanda ba a iya sake sarrafata wajen sake yin amfani da su domin hakan yana haifar da illa ga muhalli yayin da za a iya canza wannan sharar ta zama dukiya.
malam Aminu Dauda, ya ce ya yi gaggawar karbar aikin a lokacin da Zainab ta kawo wannan ra'ayi domin duk mun san cewa canza wannan gurbatacciyar sharar ta zama kalubale a duniya duk da cewa akwai karancin sake sarrafa su wanda hakan ya kara yin sanadiyyar gurɓatar muhalli fiye da kowane lokaci.
Mai kula da binciken ya ce hanyar da aka yi amfani da ita a binciken tsari ne wanda aka saba inda aka sanya sharar a ma'aunin digiri kusan 450 zuwa 500 ° C wanda ke rage karfin sinadarai da yawan zafin ruwa zuwa gajeran zango, da takaitaccen tafasasshen ruwa ba tare da anyi amfani da iskar oxygen ba.
Ya yin binciken, Malam Dauda ya ce sai da suka samar da na'ura a cibiyar fasaha dake Kano wanda aka yi amfani da ita wajen canza ledar zuwa man fetur.
Zainab wacce ‘yar asalin jihar Jigawa ce ta ce tana sha’awar yin karatu mai zurfi domin tana son ta ci gaba da binciken a karatun ta na digiri na biyu da digirin digirgir da yardar Allah, inda ta kara da cewa binciken ya lakume sama da naira 100,000.
Zainab da mai kula da binciken nata, sun yi kira ga gwamnati da ta tallfa a wannan fannin binciken domin zai sauƙaƙa yawaitar ledodi kuma a lokaci guda zai iya zama tushen samun kudaden shiga ga gwamnati da kuma hanyoyin rage zaman kashe wando ga matasa.