~Sheik Lawan Triumph
Malamin addinin musulunci a jihar Kano, Sheik Lawan Triumph, ya bayyana takaicinsa akan sabanin da aka samu a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano, tsakanin dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar NNPP, Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida) da matar shugaban hukumar tsaron farin kaya ta DSS, Aisha Yusuf Magaji Bichi, wanda rahotanni suka nuna cewa, tace indai tana raye ba zata bari Abba ya zama gwamnan Kano ba.
Triumph yace a bisa ƙai'ida ba'a shiga rikicin manya, har ya bada misali da lokacin Annabi Muhammad (S.A.W) tsakanin Abubakar da Umar, da Allah yace ba'a daga murya akan muryar ma'aiki, amma ya nemi jin abinda ya faru daga Abba, sai dai bai same shi a waya ba, amma ya bada saƙo a sanar masa yana bukatar magana dashi.
Malamin yace sunyi magana da Aisha kuma ta bayyana masa dukkan abinda ya faru, amma bazai yanke hukunci ba sai ya ji daga daya bangaren tukunna, sai dai yace duk dan kirki ba zai zagi Aisha ba, kuma tsakaninsu da ita sai fatan alheri, domin mutuniyar kirki ce.
Ya kara da cewa, yaje Abuja a kwanakin baya, suka hadu da Abba bayan ya sauka, har ya gaya masa cewa zai tafi Umrah ne, suka gaisa har sukayi hirar zumunci, kuma cikin ikon Allah a ranar Aisha ta nemi yazo gidanta yaci Abincin rana, kuma suka je tare da wasu malamai, suka yi hira da mijinta.
Suna tsaka da hirar ne aka kira wayarta, amma sai nata dauka ba, Mijinta yace ya ba za ki dauka ba? Tace dashi ai bata san me zata ce ba, domin ta bashi sunayen yara 170 da suke neman aiki, amma ya bata na mutane 100, har ta roki Malaman da su gaya masa ya dinga bata irin wannan damar idan an samu, haka dai har mijin ya tashi yace lokacin tafiya ofis yayi, a cewar Triumph.
Sheik yace akwai tarbiyya da Addini a gidan Bichi, domin ko lokacin da suka isa gidan sun tarar maigidan ya ja iyalansa sallah, saboda haka yace ba dai-dai bane a fito ana zagin Aisha ba, kuma ba akan bangaren siyasar Kwankwasiyya, ba zasu lamunci irin haka daga kowanne bangare ba.
A batun samawa matasa aiki, Malamin yace shi da kansa tare da wasu Malaman, Aisha ta basu guraben ayyuka sun bawa yara da dama.