Sau da yawa mata suna da ɗabi'ar yin ƙunshi domin kwalliya da kuma ƙawata ado sai dai a wannan lokaci anzo wata gaɓa da ƙuri'a ɗaya keda muhimmancin gaske domin da ita za iya xaɓar duk wanda ya cancanta da zai kawo wa al'umma gudunmawa.
Na'ura bata ɗaukar hannun da yake dauke da ƙunshi domin ƙunshin yana goge zanen dake hannun mutum wanda hakan ke hana na'ura mai ƙwaƙwalwa ɗaukar hannun.
mun zanta da mai magana da yawun hukumar INEC ta Kano Adam Muhammad Maulud inda ya bayyana hatsarin yin ƙunshi a irin wannan lokaci da ake ƙoƙarin shiga kakar zaɓe na wannan shekarar kuma damar yin zaɓen sau ɗaya ce idan ta wuce baza ta dawo ba.