Wakilin mu,,,,,,,,ISAH MAGAJI RIJIYA BIYU
ya rawaito mana yadda taron ya gudana.
Hakan na zuwa ne bayan da sace_sace da Shaye Shaye ya addabi unguwar ta Rijiya biyu,se al'umma da matasan unguwar suka fara tunanin yadda zasu magance matsalar.
Taron dai ya gudane a yau a unguwar ta Rijiya biyu kuma ya samu halartar ɗunbin matasa da dattawan unguwa inda kowa ya nuna goyon bayansa kan wannan aiki da aka gudanar.
Mun samu tattaunawa da wasu iyaye a unguwar da suka samu halartar taron.
Mai unguwa Sunusi Ahmad shine me unguwar ta Rijiya biyu ya jaddada goyon bayansa kan wannan al'amari inda yace duk wata gudunmawa data kamata zasu bayar don ganin unguwar sa ta zauna lafiya.
ISAH MAGAJI RIJIYA BIYU.