Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Fadar Gwamnatin Najeriya ta Aso Villa da ke Abuja.
Bayanai sun ce wannan dai ita ce ziyara ta biyu da Gwamnan Babban Bankin Kasar ya kai wa Shugaba Buhari tun bayan dawowarsa Najeriya a ranar 12 ga watan Janairu.
Wannan ziyara na zuwa ne bayan Emefiele ya halarci taron Bankin Bunkasa Tattalin Arziki na Daular Larabawa wanda Darekta Janar na bankin, Dokta Sidi Ould Tah ya jagoranta a ranar Alhamis.
Tun a bara dai labarin Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya soma yamutsa hazo bayan da aka rika rade-radin cewa jami’an tsaron na sirri na nemansa ruwa a jallo.
A makonnin bayan nan ne dai Emefiele ya bar kasar biyo bayan binciken wasu zarge-zarge da ake yi masa, da suka hada da cin hanci da rashawa da kuma samar da kudade ga ayyukan ta’addanci.
Sai dai tuni CBN ya kore wannan zargi yana mai cewa Emefiele ya ketare kasar nan saboda dalilai na hutun karshen shekara da doka ta ba shi dama.
Gabanin wannan dai, Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta nemi wata Babbar Kotun ta sahale mata cafke Emefiele, amma Alkalin kotun, M.A. Hassan ya yanke hukuncin sanya shamaki tsakanin DSS din da Emefiele.
Anya kuwa ana mulkin dimokaraɗiyya a ƙasa.