'' Maigirma Muna kira a gare ka daka fito ka bayyanawa al'ummar ƙasar najeriya hali ko matsayar da ake ciki na zargin ɓatan dabo da kuɗaɗen da aka tara daga guraben da ake karɓar Haraji na ƙasa wanda yawan su ya kai kimanin triliyan 89. Wanda ka baiwa kwamiti alhakin bincike.
Taron Gamayyar ƙungiyoyi masu zaman kansu na arewacin najeriya na jihohi 19 ciki har da birnin tarayya Abuja. Maigirma muna maka murnar shigowar sabuwar shekara kuma muna kuma taya ka murnar samun nasarar kaddamar da sabbin dokokin shekarar 2023 wanda yake ɗaya daga cikin dokokin da ƴan ƙasa ba zasu taɓa mantawa ba. Maigirma muna so muyi amfani da wannan dama na janyo hankalin ka bisa batun dake yawo na kwamitin daka naɗa ƙarƙashin jagorancin ka kan binciken nera triliyan 89 wanda sukai ɓatan dabo. A matsayin mu na ƙungiyoyi masu zaman kansu na jihohi 19 na arewa har da babban birnin tqrayya Abuja wqanda muke wakiltar al'umma
muna kira daka muna so muji yadda akai da waɗancan maƙudan kuɗaɗe wanda wasu tsirari suka wawure. Kuma muna cigaba da tura saƙƙoni da kuma ziyartar majalisa dokoki domin miƙa musu koken mu tare da al'ummar da muke wakilta. muna ƙara jin rashin daɗi bisa basussuka dake ƙara yawaita da ake bin ƙasar mu ta najeriya wani lokacin sai mu rasa gane yadda zamu rayu bisa wannan bassusuka duba da yadda ko wace shekara ake cike mana kuɗin kasafin ƙasa da bashi. Maigirma muna da labarin Hon. Gudaji Kazaure Ɗan majalisar tarayya daga jihar Jigawa cewa ka wakilta shi yana shugabantar wani kwamitee tare da Mr Adetola Adekoye daga ofishin ka domin yin binciken ƙwaƙwaf kan yadda aka nemi kuɗin rabanu na ƙasa aka rasa. Maigirma a namu tunanin akwai rashin jin daɗi matuƙa gaya da kuma zubewar kimar ƙasar mu muddin zaka cigaba da yin shiru a kan irin wannan bincike ba tare da kana saka baki ba a matsayin ka na shugaban ƙasa. Wannan batu da yake yawo bai cancanci komai ba face ka fito ka tara taron manema labarai domin ka bayyanawa al'ummar najeriya halin da ake ciki dangane da wannan badaƙala da kuma yadda aka ce an kai wasu kuɗaɗen bankunan ƴan kasuwa. Maigirma mafi muni da ɓacin ran abunda ke faruwa shine yadda gwamnati ke rantar kuɗin gwamnati kuma ake baiwa wasu shafaffu da amai kuɗin ruwa. Da wannan muke so ka dawo da duban ka guri ɗaya domin tsaftace gwamnatin ka domin tsira da mutuncin ka.
Sa hannu.....
1. Amb. Ibrahim A. Waiya – President, Kano Civil Society Forum, Kano State
2. Amb. Ibrahim Yusuf - Chairman, Association of NGOs, Gombe State
3. Amb. Idris Ozovehe Muraina - Chairperson, Kogi NGOs Network (KONGONET), Kogi State
4. Aminu Mullam – Secretary General, Network of Adamawa Non - Governmental Organizations (NANGO), Adamawa State
5. Jinjiri J. Garba – Executive Director/State Chairman, Bauchi State Network of Civil Society Organizations (BASNEC)
6. Mrs. Shimenenge Kyaagba, for: Benue Network of NGOs (BENGONET), Benue State
7. Comrade Bulama Abiso – Executive Director, Network of Civil Society Organizations Borno. Borno State
8. Muhammad Musbahu Basrika – Chairman, Network of Civil Society organizations, Jigawa State
9. Emmanuel Bonet – Chairman, Concerned civil society, Kaduna State
10. Abdulrahman Abdullahi – Chairman, Coalition of Civil Society organizations, Katsina State
11. Hon. (Dr) Usman Buhari Ali – Chairman, Coalition of NGOs in Kebbi State State (CONKS)
12. Ade Bodunde – Chairman, Kwara Forum of CSOs, Kwara State
13. Mr. Solomon Yakubu Enjola – Chairman, Nassarawa NGO Network (NANGONET), Nassarawa State 14. Habila Muhammad Kudu – Coordinator, NGOs Forum Niger State
15. Gad Peter – Rep. Coalition of NGOs Plateau State
16. Ibrahim Abdullahi Shuni – Chairman, Coalition of NGOs in Sokoto State
17. Joseph Gimba PhD – Chairman, Coalition for civil society organizations in Taraba State (COCS OTS), 18. Alh. Baba Shehu, Executive Director/Chairman, Network of Yobe Civil Society Organizations
19. Ambassador, Ibrahim Tudu – Chairman, Zamfara Coalition of NGOs (ZASCONS), Zamfara State
20. Aanu Rotimi, Chairperson – Accountability Mechanism – FCT, Abuja