Gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele yace bai fahimci alakar batun sauyin kudi da batun tsaro ba, da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yayi.
Emefiele yayin da yake amsa tambayoyin yan jarida yace baiga alakar batun sauyin kudi da kuma sha'anin tsaro a jihar Kano ba.
A baya bayannan dai gwamnan Kano ya bukaci shugaban kasa da ya dage ziyarar da ya shirya kawowa Kano,
Saboda batun tsaro dake da alaka da sauyin kudi da akeyi.
Shugaba Buhari dukda bukatar neman dage ziyarar a safiyar wannan rana ya sauka a Kano.
Hakan na zuwane bayan bankin kasa CBN ya kara wa'adin kwanaki 10 na sauyin kudi a kasar nan.
Emefiele yace baya son yayi musayar kalamai da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, domin yana kallinshi a matsayin dattijo kuma wanda yake mutuntawa.
Daga karshe Emefiele yace zasu maida hankali kan aikin dake gabansu na sha'anin kudi a fadin Najeriya.