Gwamnati ta ɓata harkar ilimi
January 04, 2023
0
Gwamnatin Najeriya ta ɓata harkar ilimi duba da yadda ɓangare biyu na malaman da ɗaliban ke kokawa yadda gwamnati ke baiwa ilimi kaso mai ƙaranci yayin ƙaddamar da kasafin ƙasa na shekara-shekara. Wannan jawabin ya biyo baya ne yayin karrama babban malami kuma Shugaban sashen tsare-tsaren karatu a kwalejin ilimi ta (Annur College of Education) wato Mal. Alh. Usman Mujittaba a duba da irin gudunmawar daya bayar a ɗaya daga cikin ƙayatattun shirye-shiryen radiyo nasar wato TUBALIN NASARA. Alh. Mujittaba Ya ƙara da cewa muddin gwamnati zata cigaba da banzantar da harkar ilimi ta hanyar ƙin amincewa da buƙatun malaman jami'o'i da kwalejojin karatu to kuwa harkar ilimi a ƙasar nan ba zata taɓa gyaruwa ba, ya kuma ce zasu zuba idanu tare da cigaba da baiwa gwamnati shawarwarin daya kamata domin a ƙara inganta ɓangaren na ilimi a ƙasar nan.
Tags