~Sen. Ahmad Lawan.
Sen. Ahmad Lawan shine shugaban majalisar Dattijai kuma kowa ya sani cewa shi a yanzu ba ɗantakara bane kasancewar yayi abunda bahaushe ke cewa ''saki reshe a kama ganye'', sannan yayi biyu babu saboda ya rasa takarar shugaban ƙasa kuma ya rasa ta sanata da yake kai a yanzu, saboda haka ko bai nemi abokin mutuwa ba to fa babu wanda zai taimakawa wajen cin zaɓen 2023, ahi yasa babu wata hanya da za'a ɓullo da ita da zai amince wadda zata fakile wannan gagarumin shiri da hukumar INEC ta yiwa wannan zaɓe mai zuwa. Mai karatu yana sane da cewa an samun canjin hanyar da za'ayi zaɓe a ƙasar nan musamman a zaɓe mai zuwa na shekarar 2023, wanda kowa ya sani cewa an saka hannu a wannan dokar majalisa ta yarda kuma za'ayi zaɓen ba tare da wasu sunyi maguɗin ƙuri'a ko ingize ba, kasancewar na'urar da za'ayi amfani da ita ta musamman ce, a saboda haka wasu sanatoci sunyi ca a kan lallai a canza wannan tsari amma anƙi kula su saboda an rigada an ƙaddamar da Dokar kuma ta tabbata, saboda muka tuntuɓi Cmr. Adam Dakata
na cibiyar wayar da kan al'umma kan kyakykyawan shugabanci da Adalci wato (CAJA) Inda ya bayyana mana cewa ''koda za'a canza ko soke ita wannan doka dole sai an bari ta kai kimanin wata 24 zuwa 25, wato shekaru biyu 2 kenan kafin a iya tunanin zaman gyara dokar a ƙaida ta kundin tsarin mulkin ƙasar najeriya, Saboda haka doka ce suka saka mata hannu suka kuma tabbatar da ita ba tare da sun karanta ta ba, saboda haka dole sai dai ayi haƙuri ko ana so ko ba'a so a bari ayi amfani da sabon tsarin da INEC tazo dashi.''