Allah ya yi wa Sarkin Dutse,
Nuhu Muhammad Sunusi rasuwa.
Kwamishinan ayyuka na musamman a Jihar Jigawa Auwal Danladi Sankara ne ya tabbatar wa shafin Raihana da rasuwar sarkin.
Sarkin ya rasu ne ranar Talata a Abuja bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya kuma ya rasu yana da shekara 79.
Sakatare na musamman na marigayin Wada Alhaji Dutse ya tabbatar wa Shafin Raihana cewa ana sa ran yin jana'izar sarkin ne a ranar Laraba a Dutse.
Kafin rasuwarsa, sarkin ya taɓa zama Uban Jam'iar Jihar Sokoto wato Sokoto State University.