Bola Ahmad Tinibu Ɗantakarar Shugabancin ƙasa ƙarƙashin tutar Jam'iyyar APC mai mulki ya koka kan yadda shugana Buhari da Gwamnan banki ke gudanar da abubuwan dake neman tunzura al'umma wanda hakan ka iya kawo targaɗo ga takarar sa musamman yayin zaɓen dake ƙaratowa. Ɗantakarar yace maimakon ace a wannan ɗan tsukukun an samarwa da al'umma sauƙi amma sai Buhari yake saɓanin haka saboda haka yake zargin akwai lauje cikin naɗ kan wannan yanayi da suka saka al'umma a ciki.