omo agege Delta Central, mataimakin shugaban majalissar dattijai, wanda ya taɓa jagorantar yan daba suka shiga majalisa domin sace Sandar majalisa wadda ita ce alamun dimokaradiyya.
Peter Nwaboshi daga Arewacin Delta, shine wanda aka taɓa yankewa hukuncin kisa amma ya tsallake rijiya da baya saboda zargin badaƙalar ɗanyan man neja dalta, kuma wani tudu wani gangare shi ke zama shugaban kwamitin man neja delta a yanzu.
Ali Ndume daga Arewacin Borno tsohon shugaban majalisar dattijai kuma yayi takara da Ahmad Ali 2019 amma ya faɗi, duk da irin jarabtar da Allah ya yiwa jihar borno na mayaƙan boko haram, amma duk lokacin da za'a ƙirga ƙuri'ar sa sai tafi ta kowa.
Ope yemi Bamidele daga jihar ikiti ta tsakiya, sanatan tshon ɗan aluta ne wanda ya shiga harkar siyasa daga baya kuma yayi kwamishina a lagos kuma yayi Ɗanmajalisar Tarayya kafin ya tafi Majalisar Dattijai, an tura shi ya dunga sa'ido a gwamnatin ikiti bayan da Feyemi Kayode ya gama tashi gwamnatin.
Ibrahim Gobir daga sakwkwato ta gabas kuma, yana da masta digiri a fannin injiniyan lantarki a jami'ar (Detroit) ta ƙasar amurka an yimai kwalliyar dakta a jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa dake jihar Bauchi yana daga cikin manyan injiniyoyin landan.
Muhammad Goje daga Gombe ta tsakiya, taohon gwamnan Gombe kuma shugaban kwamitin dace na majalisar dattijai, yayi takarar shugaban majalisar a chamber ta takwas amma daga baya ya janye bisa wani dalili daga fadar shugaban ƙasa.
Yusuf Yusuf daga Taraba ta tsakiya, yana daga cikin kwamitin Caretaker na APC, ya shiga majalisa a shekarar 2015, an ayyana shi a matsayin wanda yaci zaɓe a kotu bayan da kotu ta kori Bashir Marafa daga jam'iyyar PDP.
Ibrahim Bomai daga Yobe ta kudu, yayi aikin gwamnati a ƙarƙashin ofishin Akanta janar na ƙasa a babban birnin tarayya Abuja daga 2005 zuwa 2008 a ciki da ya kai matsayin odita kafin yayi ritaya a shekarar 2016.
Sahabi Yau daga Zamfara ta Arewa ya bar jam'iyyar PDP a ranar 21 ga Junairu 2021, yace ya yanke hukuncin ne bisa damuwar da jihar ta shiga na rikicin jam'iyya wanda canza jam'iyyar ya zame mai dole, bayan da jam'iyyar ta ƙasa ta tarwatsa tsarin da shugabancin jam'iyyar a jihar.
Uba Sani daga Kaduna ta tsakiya, ya zama mai baiwa gwamna shawara kan harkokin gwamnati a shekarar 2019, ya fito takarar sanata a shekarar 2015 kuma yaci.
Sauran sun haɗar da :
Elisha Abbo, daga Arewacin Adamawa.
Ahmad Kaita daga Arewacin Katsina
Adamu Aleru daga Kebbi ta tsakiya.
Yahaya Abdullahi daga Arewacin Kebbi.
Yakubu Oseni daga Kogi ta tsakiya.
Jibrin Isah Kogi ta Gabas.
Smart Adeyemi Kogi ta Yamma.
Ibrahim Oloruegbe Kogi ta tsakiya.
Oluremi Tinibu, Lagos ta tsakiya,
Solomon Adeola daga Lagos ta yamma.
Tanko Al-Makura daga Arewacin Nasarawa.
Godiya Akwashiki daga Nasarawa ta Kudu.
Abdullahi Adamu Nasarawa ta yamma.
Muhammad Musa daga Nija ta gabas.
Aliyu Abdullahi Neja ta Arewa.
Muhammad Enagi daga Kudancin Neja.
Noora Dadu'ut daga kudancin Plateau.
Francis Alimikhena daga Arewacin Edo.
Abubakar Kyari daga Arewacin Borno,
Ajibola daga Osun ta tsakiya. Robert
Borroffice daga Arewacin Ondo, Orji Uzo
Kalu daga Arewacin Abia, shine na goma a jerin gwanon masu kuɗin najeriya, yayi gwamna sau biyu kuma har yanzu yana fama da EFCC.
Adewole Oriolowo daga Osun ta yamma,
Aishatu Adamawa wadda aka fi sani da (Binani) daga Adamawa ta tsakiya.
Biobarakama Degi Eremiyenkamo, daga Jihar Bayelsa ta Gabas.
Oyelola Ashiru daga Kwara ta Kudu.
Bello Mandiya daga Katsina ta Kudu.
Hezekiya Dimka Plateau ta tsakiya.
Frank Ibezim daga Imo ta tsakiya.
Kashim Shettima daga Borno ta tsakiya.
Sa'ido Alƙali daga Gombe ta Arewa.
Amos Bulus daga Gombe ta Kudu.
Ɗanladi Sankara daga Jigawa ta Arewa,
Ibrahim Hadieja daga Jigawa ta Arewa.
Sulaiman Ƙwari daga Kaduna ta Kudu.
Kabir Barkiya daga Katsina ta tsakiya.
Jika Halliru daga Bauchi ta tsakiya.
Lawali Anka daga Zamfara ta Yamma.
Lawal Gumau daga Bauchi ta Kudu.
Stephen Odeh daga jihar rivers ta Arewa.
Shu'aibu Lau daga Taraba ta Arewa.