Tun farko idan kuka bibiyi tarihin waɗannan malamai da suke iƙirarin muna zubda mutuncin addini musulinci zaku ga akwai wani al'amari daya faru tsakanin mu dasu wanda muka basu Amana ta al'umma kuma suka ci, mu kuma muka dena mu'amala dasu saboda basu da abunda suke faɗe na gaskiya da rikon amana. Waɗannan ƴan izalar sune suka fi kowa surutu da kuka a kan mumbari idan sunga wani kuskure amma kuma sai ta tabbata cewa wannan kukan ba har zuciyar su yake ba domin idan an basu dama na riƙe alƙawari sai suyi shiru su daina magana ka zaci basa doron ƙasa kuma su kasa riƙe amanar da aka basu. Babu wani malami na izala da yake siyasa da aka baiwa amana ya riƙe face sai yaci wannan amanar. Da yawan waɗanda suke shiga harkar siyasa basu da riƙon amana kuma muna nan daku zamu kawo muku sunaye da video da sauran hujjoji ma waɗannan malamai na ƴan izala da suka ci haƙƙin al'ummar su. Mutanen da idan ka basu amana basa riƙewa, mutanen da suke da son zuciya, mutanen da abun duniya ne a gaban su, mutanen da basa iya kuka saboda al'umma su samu sauƙi sai dai suyi kuka don a basu amna suci.
Yanzu ku duba a ƴan takarkarun da muke dasu a wannan zaɓe mai ƙaratowa na shekarar 2023, Allah cikin ikon sa ya bamu dama mun fito da lafiyar mu, da ilimin mu, da kishin mu na Takawa da ƙasa baki ɗaya, saboda haka muka ce duk wani ɗan kishin ƙasa ya fito ya zaɓe mu domin mu samar da hanya mafi dacewa a ƙasar nan ba tare da mun bashi kuɗin zaɓe ba saboda ceto za'a taru ayi gabaɗaya, mutane suka yarda amma waɗannan Malaman ƴan izalan suka ce basu yarda ba saboda bamu da kuɗin da zamu basu, ko kuma mun ce ayi zaɓe ba don kuɗi ba, shi yasa suka zaɓi ɗan takarar da zukatan su ma ba suyi na'am dashi ba kuma suke maƙalewa da cewa wai sune suke da tsarin musulmi da musulmi wanda mu mun sani babu inda Allah ya wajabta mulki da musulunci face adalci. Shi yasa duk mulkin da yake da adalci Allah yake saka albarka a cikin sa koda kuwa bana musulmi bane, duk mulkin dake da zalunci yake cire albarka daga ciki koda kuwa musulmi ne a kai. Saboda da haka ya ragewa mutane suyi duba na tsanake su zaɓi abunda baza suyi nadama ba. Muna nan ɗauke da kashi na biyu cikin mu'amalar malaman izalal da basa ƙaunar mu samu mulki a ƙasar nan.