Professor Jibril D Jibril
malami a jami'ar Bayero daga sashen Fasaha, ya gabatar da muƙala wadda ta kunshi tarin abubuwa masu nagarta wadda ta haɗar da hanyoyin daya kamata a bi don fara gini tun daga hawa ɗaya har izuwa adadin da ake buƙata ba tare da an samu matsala.
Eng. Rabi'u Haruna shugaban ƙungiyar kwararrun magina shiyyar jihar kano.
Daya ne daga cikin manyan baki kuma ya shaidawa manema labarai cewa yana daga cikin maƙasudin wannan taro kamar yadda farfesa ya gabatar da talarda innda ya bayyana yadda al'umma za suyi gini ciikin farashi mai sauƙi kuma mai nagarta , kuma hakan zai taimakawa gwamnati wajen samun kuɗin shiga domin maimakon a dunga siyo kaya daga waje sai dai ake siya a cikin gida.
Shima a nashi jawabin shugaban nasu
Magini Mahmud Sa'id
ya bayyana irin tasirin da wannan mukala da aka gabatar zata kawo na cigaba mai É—orewa a faÉ—in jihar kano, sannan duk wata hanya da doka ta tanadar musu da subi don hukunta masu É“ata musu suna za subi bayan ya shawarce su da su koma subi da duk ya kamata ace magini yabi kafin ya zama magini domin gujewa kuskure mafi girma a rayuwa.
Bayan wannan takarda da aka gabatar awai pro gwanon waÉ—anda aka karrqma bisa gudunmawa da suke baiwa wannan tafiya da kuma jajircewa wajen gudanar da aikin su na yau da gobe daya shafi al'umma .