A wannan Rana ta litinin Shugaban Kasa Buhari yaziyarci Jahar Kano indaya taso daga mahaifarsa ta Daura dake jihar Katsina, inda zai kaddamar da ayyuka da dama a jihar Kano.
Ayyukan da zai kaddamar sun hada da.
1. kaddamar da wutar lantarki da adadinta ya kai Megawatt 10.
2. Kaddamar da tashar tsandauri ta Dala Dry port.
3. Kaddamar da cibiyar adana muhimman bayanai ta Kano.
4. Kaddamar da kamfanin galaxy backbone.
5. Kaddamar da cibiyar yaki da cutar kansa a Asibitin Giginyu.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kuma ziyarci fadar mai martaba sarkin Kano, sannan ana sa rai zai kaddamar da karin wasu ayyuka daga cikinsu har da babbar gada da gwamnatin Kano ta sanyawa suna Muhammadu Buhari.