Gwamnatin Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta sanar da dage bikin bude manyan ayyuka, musamman gadar shataletalen Hororo da kuma kasuwar zamani ta Dangoro, wacce aka gayyaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bude.
Shugaban karamar hukumar Nasarawa, Auwal Lawan Shu'aibu (Aranposu) ne ya tabbatar da hakan, cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumunta, yana mai cewa an dage bikin bude ayyuka zuwa wani lokaci nan gaba.
A ranar Litinin mai zuwa ne aka tsara cewa shugaban zai ziyarci Kano domin wadancan ayyuka, kafin daga bisani kuma a soke ziyarar.