Hajiya Naja'atu Muhammad, ta jaddada goyon bayanta ga dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar NNPP mai alamar kayan marmari, Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida), a babban zaɓen shekarar 2023 da ke tunkarowa, amma tace a sama, wato dan takarar shugaban, jam'iyyar PDP za ta yi, domin goyon bayan Alhaji Atiku Abubakar Wazirin Adamawa.
Naja'atu, wacce mamba ce a hukumar kula da ayyukan yan sanda ta ƙasa, tace a yanzu ta fahimci cewa duk jam'iyyun siyasa kalarsu daya, shi yasa ta ga dacewar goyon bayan dan takara ba jam'iyya ba, kuma ta san cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bai shiryawa yan Nigeria komai ba, shi yasa tayi masa bankwana.
A jawabin da ta gabatar bayan ajiye mukamin daraktar yaƙin neman zaɓen Tunibu a bangaren mata, da kuma ficewarta daga jam'iyyar APC, Naja'atu tace tana so tayi siyasar ra'ayi da 'yanci, shi yasa yanzu bata wata jam'iyyar ba, illa kawai goyon bayan yan takarar da ta ke ganin sun cancanta, gudun kada ace tayi munafurci, bai kamata tana cikin jam'iyya kuma ta goyi bayan dan takarar wata jam'iyyar ba.
Bugu da ƙari, tace a jihar Adamawa, tana goyon 'yar takarar gwamna ta jam'iyyar APC, Aisha Binani, don haka ne ta ke kira ga yan Nigeria, da su tabbatar sunyi amfani da 'yancinsu su zaɓi Mutanen da suka cancanta a kowacce jam'iyya.