Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙaramar hukumar Nasarawa Hon. Nasir Ali Ahmad, kuma shugaban kwamitin kula da tsare-tsare na harkokin ma'aikatun gwamnati ya raba OFFER ta aiki a matakin gwamnatin Tarayya kimanin guda ashirin da biyu.
wannan dai ba shine karo na farko ba kuma ba shine na biyu ba, ya raba fiye da haka a baya. Yayin gudanar da taron shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Nasarawa Salisu Ayo Gawuna
ya bayyana cewa ''shi wannan Ɗanmajalisa mutum ne da yake ƙaunar ganin ɗan talaka yana gogayya da ƴaƴan masu kuɗi duba da yadda yake samar musu aiki a ma'aikatun da iya ƴaƴan masu kuɗi ake kaiwa kuma wannan karon a jimalar OFFER ta aiki daya bayar ta kai kimanin 215 saboda haka yana kira ga ƴaƴan ƙaramar hukumar Nasarawa su kuma zaɓen sa karo na huɗu domin ya cigaba da kawo musu makamantan wannan ayyuka na cigaba koma fiye da haka musamman ifan Allah ya bashi kujerar kakaki na ƙasa.
A nashi jawabin
Ya bayyan taron a matsayin taron ''Ala tsine uwar mai ƙarya'' domin rana ce da Wakilin al'umma zai nuna aikin daya yiwa al'ummar sa na cigaba ta yadda idan ya buƙaci su zaɓe shi to fa babu tantama zasu kuma zaɓar sa koda kuwa karo na biyar ne ba na huɗu ba sannan kada su sake su zaɓi wani ba shi ba domin zasu tafka babban kuskure su kuma yi nadama, wannan dai ba shine karo na farko ba ballantana ƴan adawa su ce sai da aka ga zaɓe ya ƙarato sannan aka saki wannan OFFERS ba.
A nashi jawabin Mai gayya mai aiki
Hon. Nasir Ali Ahmad yayi kira ga al'ummar ƙaramar hukumar Nasarawa dasu kasance masu lura musamman yayin gudanar da zaɓen shekarar 2023, kuma tun a lokacin da suka zaɓe shi bashi da wani buri daya wuce ganin ɗantalaka ya zamo abun misali a ƙasa kuma suna gogayya da manya wajen kawo cigaban ƙasa. a cikin ma'aikatun gwamnatin tarayya 802 babu wadda baza a samu ƴaƴan ƙaramar hukumar Nasarawa suna aiki a ciki ba. sabida son shi da ganin sun samu aikin yi da kuma tabbatar da taken kafen ɗin sa na ''NASARAWA BA JAGALIYA'' da kuma ''MU GANI A ƘASA.''
Musa Dambele (Jagari Mai Feshin Wuta Irin ta Siyasa) guda ne daga cikin sojojin baka na gidan Nasir Ali Ahmad kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka rabauta da OFFER ta aiki a gidan inda ya bayyana farin cikin sa da samun wannan dama da kuma godiya ga Allah bisa rabauta da wannan dama na samun aiki a babbar ma'aikatar gwamnatin Tarayya, (Ma'aikatar Kula da saukan jiragen sama ta ƙasa).ya kuma ce yanzu ya fara bashi gudunmawa a siyasance. Haka shima
Nazir ÆŠanhalak
wanda guda ne a cikin Æ´an midia na gidan wanda ya rabauta da OFFER ya nuna nashi farin ciki da kuma godiya ga Allah tare da É—aukar alwashin cigaba da baiwa wakilin gudunmawa.
Hassan Gwari
A dai wajen taron ƙungiya mai zaman kanta ta karrama Ɗan Majalisar Tarayya bisa jajircewar sa na ganin ya samawa Ɗantalaka aiki.