Jam'iyyar NNPP ta ƙaddamar da kwamitin kula da asusun tallafi na yakin neman zaɓe na shekarar 2023.
Takardar mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun Ɗantakarar Shugabancin Ƙasa dana Gwamnan Jihar Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa,
inda yace kwamitin zai samh shugabancin gogaggen ɗan siyasa, ɗan kasuwa, kuma tsohon mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai ta ƙasa
Hon. Dr. Sulaiman Abdurrahman Kawu Sumaila.
Yayin Bikin ƙaddamar da mambobin kwamitin asusun a sakatariyar jam'iyyar ta sharaɗa, shugaban kamfen na NNPP na Kano Gwani DR. Ali Abubakar Haruna Makoda ya bayyana tsohon shugaban gidauniyar karatu ta TETFUND
Dr. Abdullahi Baffa Bichi a matsayin mataimakin chiyaman, tare da
Eng. Nura Hussain Na'abba da
Sunusi Bature Dawakin Tofa a matsayin Sakatare kuma mataimakin Sakatare. Sauran mambobin sun hadar da:
Alh. Adamu A.Y. Maikifi,
Dr. Kassim Batayya,
Alh. Dayyabu Ahmad Maiturare,
Alh. Gambo Ɗanpass,
Sen. Rufa'i Sani Hanga,
Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum,
Alh. Garba Hungu,
Nasir Danfaranshi, da
Wali Danchana.
Haka kwamitin kuɗin yana ɗauke da Hon. Tijjani Abdulƙadir Jobe,
Hon. Badamasi Ayuba,
Dr. Abdulmumin Jibril Kofa,
Rt. Hon. Isyaku Ali Ɗanja,
Hon. Lawan Hussain da
Rt. Hon. Zubairu Hamza Massu duk a matsayin mambobi.
Yayin gabatar da jawabin sa Ɗantakarar Gwamanan Jihar Kano ƙarƙashin tutar Jam'iyyar NNPP Eng. Abba Kabi Yusuf (ABBA GIDA-GIDA), ya bayyana zaɓin
Hon. Kawu a matsayin wata fikira da Allah ya hore masa musamman a fannin siyasa. Sannan ya cigaba da cewa ''muna cikin hannun tsira kuma mun tabbata babu wani nakasu da za'a samu a ƙarƙashin jagorancin sa '' sannan yayi kira da kuma fatan cewa waɗannan mambobi za suyi biyayya ga wannan shugabanci sannan su girmama matsayin ƴan takarkarun biyu na sama dana ƙasa.
A jawabin sa Hon. Kawu Sumaila shugaban wannan kwamiti na kula da asusun tara kuɗaɗe ya bayyana ranar 4 ga watan faburairu a matsayin ranar daza a ƙaddamar da wannan asusu da kuma fara saka masa kuɗaɗe a kano.