Idan masu bibiyar mu suna tare damu sun suna sane da cewa akwai lamarin da yake faruwa na ƴan kwankwasiyya da wasu da suke zargin suna shirya musu bita da ƙulli a cikin zaɓe me ƙaratowa kamar yadda suke iƙirarin an kwace musu zaɓen shekarar 2019. Kwatsam sai aka ji wata mata Mai suna Aisha Magaji matar shugaban ƴandandan farin kaya na ƙasa,, wadda tayi suka ga takarar ABBA GIDA-GIDA, a filin saukar jirgi na Malam Aminu Kano, dake kano. Wanda dalilin haka ne ya janyo cece-kuce tsakanin ƴan kwankwasiyya da ita da kuma magoya bayan ta. A cikin magoya bayan nata an samu wasu malamai inda suka fito suna kare ta suna faɗin tana da kirki bai kamata aci mutuncin ta ba. Wanda hakan ya tunzura wasu ƴan kwankwasiyyar kuma suke maida martani daban-daban.
Wannan shine dalilin da yasa
Mal. Musa Yusuf
ke da'awa inda yake nuna rashin dai-dai na ƴan Kwankwasiyya bisa zagi na waɗancan malamai daya ce suna yi inda ya danganta hakan da cewa suna shiga rigar sa kuma suna taka mutane masy daraja, a ƙarshe yayi kira da Kwankwaso ya tsawatar musu dasu daina irin wannan ɗabi'a.