Rahotanni sun bayyana cewa, an samu rikici a masallacin Darul Hadith na Marigayi Dr. Ahmad BUK a yau juma’a, bisa jagorancin masallaci.
Rikicin ya faru ne yayin da sabon Liman zai hau Mumbari domin fara HuÉ—ubar juma’a, sai wasu fusatattu suka janyo rigarsa ta baya don nuna Æ™in amincewa da shi.
Tuni dai aka rufe masallacin wanda yake a Unguwar Tudun Yola dake birnin Kano, tare da baza jami’an tsaro a kofa da kewayensa.