Inda yace yana zaune wani mutum yazo yake tambayarshi gidan wani mutum mai suna Sani Dansanda data rasu acewar mutumin yar Sani Dansanda ce tayarda da wasu muhimman takardu na makaranta ta jami'ar bayero
Shikuma dattijo yace yasani wani mai iron sunan amma shi yana nan baimutu ba, sai yace amma muje mubincika ko Allah zaisa adace, sai da sukayi nisa suna tafiya sai mutumin nan yacewa dattijon "Afuwan mantawa nayi matarshi ce tarasu mai maigidan ba"
Sai yace sujiyo kawai yazaro Dari biyu 200 yabawa dattijo har dattijon yatafi sai mutum yakwalla mishi kira yajiyo sai yace mishi baba ko kana da asusun ajiyar kudi sai yace a'a bashi da shi.
Sai yace to zanbudema saboda zansamarma aiki dattijo yace wanne irin aiki sai yace mishi aikin digon baki na foliyo, sai dattijo yace nikam taya zan iya aiki bayan banyi karatu ba, sai yace karkadamu zansan yadda za'ai.
Sai yacewa Dattijo kana da Dari Biyar 500 sai yace eh ita kadai nake da ita sai yace bani daya bashi sai shikuma yabashi Hamsin daga aljihunshi bayan yasa Dari Biyar acikin aljihu, sai yace bani katin shidar dankasanka da katin za6enka duk yahada yabashi,
Sai yace yabashi lambar wayarshi zaikira shi da dare yayi yakirashi sai yace kasamo min Dubu Uku zanhadama komai, sai yace bashi da kudi dan haka shi yama fasa aikin yadawo mishi da katin zabenshi da katin shaidar dan kasanshi, sai yace zaidawo mishi da shi da Dari Biyar dinma.