Shi chanjin kudin ba shine matsala ba, matsalar shine a bar alumma su kashe na hannun su a hankali har sabbin su wadaci al'umma ~Murtala Sule Garo
Tsohon kwamishinan ƙananun hukumomi na Jihar Kano kuma mataimakin Ɗantakarar Gwamnan jihar kano ƙarƙashin tutar jam'iyyar APC Alh. Murtala Sule Garo ya bayyan rashin jin daɗin sa bisa wannan lamari da jama'a ke ciki na rashin jin daɗi bisa wannan canjin kuɗi da Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamnan Banki ke ƙoƙarin saka mutane a ciki. Ya kuma bayyana cewa idan har don al'umma za ayi wannan to su sani su basa son wannan kuma baza su yarda da hakan ba.