Wata Jiha a Australia,ta amince da canja tsarin halitta ba tare da neman izinin iyaye ba.
Gwamnatin
(Annastacia Palaszczuk's)
ita ce jiha ta farko a ƙasar Australia data bada damar matasa sun dunga canza tsarin halittar su daga mace zuwa Namiji ko daga Namiji zuwa mace don haka duk lokacin da aka haifi jariri a jihar a wajen cike masa takardar haihuwa ya zama zaɓi wajen rubuta tsarin halittar sa wato ba dole bane.
Wannan tsarin ku san shine na biyu bayan da jihar Tasminia ta fara amincewa da tsarin tun a shekarara 2019 kamar yadda wata majiya mai ƙarfi ta bayyanawa shafin raihana.com.ng.
Kafin yanzu duk wanda yake da niyyar canza tsarin halittar sa sai ya tuntuɓi iyayen sa kuma sai sun amince kasancewar su wanda suka haife su.
Haka matasa daga shekaru 16 zasu iya fara jima'i da duk wanda suka ga dama ba tare da neman yardar iyayen su ba.
Su kuma ƴan shekaru 12 zuwa 15 doke sai sun nemi yardar iyayen su kafin fara jima'i ko canza tsarin halittar su, amma zasu iya kai ƙara kotu idan iyayen su sun hana su kuma basu gamsu da shawarwarin iyayen su ba.
haka ba za'a buƙaci bayanai daga gurin likitoci ko masana halayyar ɗan Adam ba yayin da ɗan ƙasa yaso canza tsarin halitta ko fara jima'i a matsayin matashi ba.
Abu ne da Yammacin Australia ta amince dashi kuma an ƙaddamar dashi a kudancin ƙasar da kuma Arewacin ta.
Duk da yarda da amincewa da kotun ƙasar tayi na wannan tsarin, ta gargaɗi masu sha'awar canza tsarin halittar su inda tace musu abu ne mai hatsarin gaske kuma ka iya kaiwa ga kai ƙarar likitocin da suke wannan aiki a kotu muddin aka samu tangarɗa