'Yan kasuwar Kwari da ke jihar Kano, sun koka kan yadda harkokin cinikinsu ya ja baya, sakamakon yadda wa'adin daina karɓar tsofaffin Kuɗin Naira (N1000, N500, N200) ke cigaba da karatowa
Toni dai wasu yan kasuwar suka fara sanar da abokan huldar su cewa za su daina karbar tsofaffin kudin daga wannan rana ta Asabar, yayin da wasu kuma suka ambata ranar Litinin mai zuwa da kuma Talatar makon gobe ko Laraba, sai dai a tura musu ta asusun ajiya na banki (transfer).
Yan kasuwar ta bakin sakataren ƙungiyar masu sana'a a waje ta kantin kwari, Musa Arzai, ne bayyana haka ga manema labarai, inda yace suna bukatar a ƙara wa'adin daina karɓar tsofaffin Kuɗin da babban bankin Nigeria CBN ya ayyana ranar 31 ga watan da muke ciki na Janairu a matsayin cikar wa'adi.
Toni dai al'umma sukace babban baking na CBN natura salon karta kwana a wayoyinsu domin kara gargadarsu da cewar wannan dokarfa nan daram