Majalisar dattijan Najeriya, sun tafi hutu a Larabar data gabata, domin samun cigaba da gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓe a jam'iyyun da suke ciki, don tunkarar babban zaɓen shekarar 2023, kamar yadda shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana yayin zaman majalisar a jiyan.
Sanata Ahmad yace zace zasu tafi hutun ne domin tabbatar da abubuwa sun zama cikin tsari a ƙasar nan,
kuma za su dawo a ranar 28 ga watan Fabrairu, kwanaki uku kenan bayan an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa dana yan majalisun tarayya, kafin su sake tafiya wani hutun a ranar 1 ga watan Maris, domin gudanar da zaɓen gwamnoni da yan majalisun dokokin jiha, da za'ayi a ranar 11 ga watan Maris.
Cikin jawabinsa, Sanata Ahmad Lawan yayi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, da kuma jami'an tsaro, akan su tabbatar sunyi ayyukansu yadda ya dace, domin yin zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana, karbabben zaɓe kuma sahihi.