A kalla mutane 25 sun riga mu gidan gaskiya a Kano sakamakon kamuwa da cutar diptheria.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Aminu Tsanyawa, ne ya bayyana haka, inda yace a kalla mutum 25 sun rasu.
Kwamishinan wanda ya tabbata da bular cutar a ranar Alhamis ya ce jihar a shirye ta ke don daukan matakan magance cutar, yana mai cewa an kafa cibiyar magani kuma ana sa ido.
Alamomin cutar sun hada da ciwon makogoro, tari, zubar da yawu, sauyawan murya, kumburin wuya, wuyar numfashi, zazzabi ko warin baki da sauransu.
Masana sun ce, cutar tana tokare kafar shige da ficen iska kuma ta hana mai ɗauke da ita yin numfashi, har ma a ƙarshe ta kashe shi.
Yin magani cikin gaggawa yana da matuƙar amfani domin kiyaye mai ɗauke da wannan cuta daga mutuwa ko naƙasa. Cuta ce da take bin iska, don haka tana yaɗuwa ta hanyar tari, atishawa ko haɗa jini da mai ɗauke da ita.