Umarnin ya biyo baya ne bayan da Sanata Sadiq Sulaiman na Jam'iyyar APC mai wakiltar Kwara ta arewa ya kawo na a dakatar da babban bankin ƙasa da karɓar tshon kuɗi don sauƙaƙawa al'umma kasancewar sun shiga firgici mai tsanani a yanzu haka. Sai dai CBN tasha alwashin tabbatar da dena mu'amala da wannan tsohon kuɗi daga ranar 31 ga wannan wata na junairu da muke ciki.
Takwarorin sa sun mara masa baya bisa wannan kudiri face Sanata Sam Egwu na jam'iyyar PDP daga jihar EBONYI ta Arewa
tun a baya dai babbar chamba ta baiwa CBN shawara kan su tsagaita wannan rana amma sukayi kunnen uwar shegu.
Zamu kawo muku cigaban wannan rahoto daga majalisar ta Dattijai.......