Naja’atu Mohammed tayi murabus daga kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban Æ™asa a karkashin jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, kuma nan take ta fice daga jam'iyyar.
Naja'atu ta bayyana haka ne cikin wata wasika da ta aikewa shugaban jam'iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, da kuma shugaba na mazabar Shahuci a karamar hukumar Birni dake jihar Kano.
A cewar Dr Naja'atu Bala Muhammad "Babu bambamci a tsakanin jam'iyyun siyasa a Nigeria, duk kanwar ja ce"
Hajiya Naja’atu Mohammed, wacce yanzu haka Kwamishina ce a Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan sanda a Najeriya, ta ce kalubalen da kasar nan ke fuskanta a yanzu ya sanya dole ta fito daga takunkumin duk wata jam’iyya don ta shiga gwagwarmayar kai kasar nan zuwa tudun tsira.
Naja’atu ta sanar da ficewarta daga jam'iyyar APC, cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 19 ga Janairun 2023, wadda ta aike wa Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu.
A wata sanarwa da fitar a wannan Asabar din, Naja’atu ta ce duk jam’iyyyu a fadin kasar nan ba su da wani bambancin akida.
Ta bayyana ta cewa jam’iyyun kasar kamar tufafi mabanbanta da ’yan siyasa sukan saka don wata bukata ta kansu kebantacciya.
’Yar siyasar ta ce ta mayar da hankali wurin goyon bayan jama’a da ke da burin shawo kan matsalar kasar nan tun daga tushe a Najeriya.