Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta sanar da cewa tana kan tattaunawa da kamfanin Meta masu mallakin Facebook, WhatsApp da kuma Instagram, domin dakile yaduwar labaran ƙarya a yayin babban zaɓen shekarar 2023.
Jawabin hakan ya fito ne daga bakin daraktan Ilimintar da al'umma akan zaɓe da kuma yada labarai, Victor Aluko, inda yace zasu yi duk mai yiwuwa wajen ganin ba'a samu yawaitar yaɗa labarai marasa tushe a zaɓen 2023 ba.