Wakilan zauren hadin kan Malaman Addinin musulunci ce ta shigar da korafi akan yada batsa, zage-zage da rashin tarbiyya ga Murja Ibrahim Kunya. Murja dai Matashiya ce data shahara wajen yin tik tok inda take gabatar da ire-iren tarbiyya da ɗabi'un da take dasu a shafin. Tun a baya anyi kira ga malamai dasu ɗauki mataki a kan wannan halin rashin tarbiyya da take nunawa a shafin na tik-tok, sai wannan lokaci ne malaman suka farga suka kuma nuna fushin su tare da shigar da ita ƙara gaban kuliya manta sabo inda suka buƙaci kotun ta ɗau mataki a kanta.
Tuni da kotun ta tura aje a gwada ƙwaƙwalwar ta don tabbatar da tana da lafiya ko akasin haka.